6 Nayara ta haifa masa Ahuzzam, da Hefer, da Temeni, da Hayahashtari. Waɗannan su ne 'ya'yan Nayara, maza.
7 'Ya'yan Hela, maza, su ne Zeret, da Izhara, da Etnan.
8 Hakkoz shi ne mahaifin Anub, da Zobeba, shi ne kuma kakan iyalin da suka fito daga zuriyar Aharhel ɗan Harum.
9 Yabez ya fi sauran 'yan'uwansa kwarjini saboda haka mahaifiyarsa ta sa masa suna Yabez, wato da wahala ta haife shi.
10 Yabez ya roƙi Allah na Isra'ila, ya ce, “Ka sa mini albarka, ka faɗaɗa kan iyakata, hannunka kuma ya kasance tare da ni, ka kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni.” Allah kuwa ya biya masa bukatarsa.
11 Kalibu ɗan'uwan Shuwa, shi ne mahaifin Mehir wanda ya haifi Eshton.
12 Eshton kuwa shi ne ya haifi Bet-rafa, da Faseya, da Tehinna wanda ya kafa birnin Ir-nahash, zuriyar waɗannan mutane kuwa su suka zauna a Reka.