9 Ya kuma zauna wajen gabas, har zuwa goshin jejin da yake wajen Kogin Yufiretis, saboda shanunsu sun ƙaru a ƙasar Gileyad.
10 Zuriyar Ra'ubainu suka yi yaƙi da Hagarawa a kwanakin Saul. Suka ci Hagarawa, saboda haka suka zauna a ƙasar da take gabashin Gileyad.
11 'Ya'yan Gad, maza, suka zauna a ƙasar Bashan, daura da Ra'ubainawa har zuwa Salka.
12 Yowel ne sarki, Shafam kuwa shi ne na biyun, da Yanai, da Shafat, su ne tushen Bashan.
13 Danginsu bisa ga gidajen kakanninsu, su ne Maikel, da Meshullam, da Sheba, da Yorai, da Jakan, da Ziya, da Eber, su bakwai ke nan.
14 Waɗannan su ne 'ya'ya maza na Abihail ɗan Huri. Ga yadda kakanninsu suke, wato Abihail, ɗan Huri ɗan Yarowa, ɗan Gileyad, ɗan Maikel, ɗan Yeshishai, ɗan Yado, ɗan Buz.
15 Ahi ɗan Abdiyel, wato jīkan Guni, shi ne shugaban gidan kakanninsu.