75 da Helkat duk da makiyayarta, da Rehob duk da makiyayarta.
76 Daga na kabilar Naftali kuma an ba da Kedesh ta Galili duk da makiyayarta, da Hammon duk da makiyayarta, da Kartan duk da makiyayarta.
77 Daga na kabilar Zabaluna, an ba sauran Lawiyawa, wato 'ya'yan Merari, maza, Rimmon duk da makiyayarta, da Tabor duk da makiyayarta.
78 Daga na kabilar Ra'ubainu a hayin Urdun a Yariko, wato gabashin Urdun, an ba da Bezer ta cikin jeji duk da makiyayarta, da Yahaza duk da makiyayarta,
79 da Kedemot duk da makiyayarta, da Mefayat duk da makiyayarta.
80 Daga na kabilar Gad kuma an ba da Ramot ta Gileyad duk da makiyayarta, da Mahanayim duk da makiyayarta,
81 da Heshbon duk da makiyayarta, da Yazar duk da makiyayarta.