11 da Azariya ɗan Hilkiya, shi ne jami'in Haikalin Ubangiji, kakanninsa sun haɗu da Shallum ɗan Zadok, da Merayot, da Ahitub,
12 da Adaya ɗan Yeroham, kakanninsa sun haɗu da Fashur, da Malkiya, da Ma'asai ɗan Adiyel, kakanninsa sun haɗu da Yazera, da Meshullam, da Meshillemot, da Immer.
13 Firistacin da suke shugabannin gidajen kakanninsu, sun kai mutum dubu da ɗari bakwai da sittin (1,760). Ƙwararru ne cikin hidimar Haikalin Ubangiji.
14 Lawiyawa masu zama a Urushalima kuma, su ne Shemaiya ɗan Hasshub, wanda kakanninsa suka haɗu da Azrikam da Hashabiya daga 'ya'yan Merari, maza,
15 da kuma Bakbakkar, da Heresh, da Galal, da Mattaniya ɗan Mika wanda kakanninsa su ne Zikri da Asaf,
16 da kuma Obadiya ɗan Shemaiya, kakanninsa su ne Galal da Yedutun, da Berikiya ɗan Asa, wato jīkan Elkana, wanda ya zauna a garin Netofa.
17 Masu tsaron Haikalin, su ne Shallum, da Akkub, da Talmon, da Ahiman, da 'yan'uwansu. Shallum shi ne shugaba.