2 Waɗanda suka fara zama a biranen mallakarsu, su ne Isra'ilawa da firistoci, da Lawiyawa, da kuma ma'aikatan Haikali.
3 Waɗansu mutanen Yahuza, da na Biliyaminu, da na Ifraimu, da na Manassa suka zauna a Urushalima.
4-6 Iyalin Yahuza guda ɗari shida da tasa'in suka zauna a Urushalima, shugabansu kuwa shi ne Utai ɗan Ammihud, jīkan Omri daga wajen Feresa. Waɗansu kakanninsu kuwa su ne Imri da Bani. Zuriyar Shela ɗan Yahuza suna da shugaba mai suna Asaya. Zuriyar Zera ɗan Yahuza kuwa, shugabansu Yuwel.
7 Ga zuriyar Biliyaminu a Urushalima bi da bi, da Sallai ɗan Meshullam, da Hodawiya, da Hassenuwa,
8 da kuma Ibneya ɗan Yeroham, da Ila ɗan Uzzi, wato jīkan Mikri, da Meshullam ɗan Shefatiya, da Reyuwel, da Ibnija.
9 Tare da danginsu a zamaninsu, sun kai ɗari tara da hamsin da shida ne. Duk waɗannan shugabannin gidajen kakanninsu ne.
10 Daga cikin firistoci masu zama a Urushalima su ne Yedaiya, da Yehoyarib, da Yakin,