35 Yehiyel ne ya kafa Gibeyon ya zauna a ciki, sunan matarsa Ma'aka,
36 ɗan farinsa kuma shi ne Abdon. Sa'an nan ga Zur, da Kish, da Ba'al, da Ner, da Nadab,
37 da Gedor, da Ahiyo, da Zakariya, da Miklot,
38 mahaifin Shimeya. Zuriyarsu ne suka zauna a Urushalima daura da 'yan'uwansu.
39 Ner ya haifi Kish, Kish kuma ya haifi Saul, Saul ya haifi Jonatan, da Malkishuwa, da Yishwi, da Ish-boshet.
40 Jonatan ya haifi Mefiboshet, Mefiboshet ya haifi Mika.
41 'Ya'yan Mika, maza, su ne Fiton, da Melek, da Tareya, da Ahaz.