38 Kada su manta da alkawarin da ya yi da su, kada kuma su ji tsoron gumaka.
39 Amma su yi tsoron Ubangiji Allahnsu, shi kuwa zai cece su daga hannun dukan abokan gābansu.
40 Duk da haka ba su kasa kunne ba, amma suka yi kamar yadda suka saba yi tun dā.
41 Waɗannan al'ummai suka yi wa Ubangiji sujada, amma suka kuma yi ta bauta wa gumakansu. Haka kuma 'ya'yansu da jikokinsu suka yi kamar yadda kakanninsu suka yi. Haka suke yi har wa yau.