1 Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan Isra'ilawa sun tafi don su naɗa shi sarki.
2 Da Yerobowam ɗan Nebat, ya ji wannan labari (gama a Masar yake sa'ad da ya guje wa sarki Sulemanu), Yerobowam kuwa ya komo daga Masar.
3 Aka aika a kira shi, sai Yerobowam da dukan Isra'ilawa, suka je wurin Rehobowam suka ce,
4 “Tsohonka ya tsananta mana, yanzu sai ka sawwaƙa mana irin tsananin da muka sha daga wurin tsohonka, da irin tilastawar da ya yi mana, sa'an nan sai mu bauta maka.”
5 Rehobowam kuwa ya ce musu, “Ku komo bayan kwana uku.” Sai jama'a suka tafi.
6 Rehobowam ya nemi shawara a gun dattawan da suke tare da tsohonsa Sulemanu, sa'ad da yake da rai, ya ce, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa jama'ar nan?”