4 Ya umarci Yahuza su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu, su kiyaye doka, da umarni.
5 Daga cikin dukan biranen Yahuza, ya kawar da masujadai da bagadan ƙona turare. A zamaninsa an sami zaman lafiya a mulkinsa.
6 Ya giggina birane masu kagara a Yahuza, gama ƙasar tana zaman lafiya. A waɗannan shekaru bai yi yaƙi da kowa ba, saboda Ubangiji ya kawo masa salama.
7 Sai ya ce wa mutanen Yahuza, “Bari mu giggina waɗannan birane, mu kewaye su da garu, da hasumiya, da ƙofofi masu ƙyamare. Ƙasar tamu ce har yanzu, saboda mun nemi Ubangiji Allahnmu. Mun neme shi, ya kuwa ba mu salama a kowace fuska.” Suka yi ta gini, suka kuwa arzuta.
8 Sarki Asa kuwa yana da soja dubu ɗari uku (300,000) a Yahuza, ko wanne yana da kutufani da māshi, yana da soja dubu ɗari biyu da dubu tamanin (280,000) daga Biliyaminu, 'yan baka ko wanne da garkuwarsa. Dukansu manyan jarumawa ne.
9 Sai Zera mutumin Habasha ya zo da soja zambar dubu (1,000,000) da karusa ɗari uku har Maresha, don ya yi yaƙi da su.
10 Don haka sai Asa ya fito ya gamu da shi, suka kuwa jā dāga a kwarin Zefata a Maresha.