1 A shekara ta talatin da shida ta mulkin Asa, sai Ba'asha, Sarkin Isra'ila, ya haura ya fāɗa wa Yahuza da yaƙi, ya gina Rama don ya hana kowa fita, ko shiga wurin Asa, Sarkin Yahuza.
2 Sa'an nan Asa ya ɗebo azurfa da zinariya daga dukiyar da take cikin Haikalin, da na fādar sarki, ya aika wa Ben-hadad da su, wato Sarkin Suriya, wanda yake zaune a Dimashƙu, yana cewa,
3 “Bari mu haɗa kai, da ni da kai kamar yadda ubana da naka suka yi. Ga shi, na aika maka da azurfa da zinariya. Ka tafi ka warware haɗa kan da yake tsakaninka da Ba'asha, Sarkin Isra'ila, don ya janye ya rabu da ni.”
4 Ben-hadad kuwa ya kasa kunne ga sarki Asa, ya aika da shugabannin rundunan sojojinsa suka yi yaƙi da biranen Isra'ila. Suka ci Iyon, da Dan, da Abel-bet-ma'aka, da dukan biranen ajiya na Naftali.
5 Da Ba'asha ya ji haka, sai ya daina gina Rama, ya bar aikin da yake yi.
6 Sa'an nan sarki Asa ya kawo dukan mutanen Yahuza, suka kwashe duwatsun da katakan da Ba'asha yake gina Rama da su, ya gina Geba da Mizfa da su.