1 Yehoshafat ɗansa kuwa ya gāji gadon sarautarsa, ya kahu sosai gāba da Isra'ila.
2 Ya sa sojoji a kowane birni mai kagara a Yahuza, ya kuma sa ƙungiyoyin sojoji masu tsaro a ƙasar Yahuza, da kuma a biranen Ifraimu waɗanda tsohonsa Asa ya ci da yaƙi.
3 Ubangiji kuwa yana tare da Yehoshafat saboda ya bi halin tsohonsa da ya yi da fari, bai kuwa nemi Ba'al ba.
4 Ya nemi Allah na ubansa, ya bi umarnansa. Bai bi halin Isra'ila ba.