19 Sai Ubangiji ya ce, ‘Wa zai ruɗi Ahab, Sarkin Isra'ila, don ya haura zuwa Ramot-gileyad ya fāɗi?’ Sai wannan ya faɗi abu kaza, wancan kuma ya faɗi abu kaza.
20 Sai wani ruhu ya zo ya tsaya a gaban Ubangiji, ya ce, ‘Ni zan ruɗe shi.’ Sai Ubangiji ya ce masa, ‘Ta ƙaƙa?’
21 Sai ya ce, ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakin dukan annabawansa.’ Sa'an nan Ubangiji ya ce, ‘To, za ka ruɗe shi har ka yi nasara. Je ka, ka yi haka nan.’
22 “Saboda haka Ubangiji ya sa ruhun ƙarya a bakunan annabawanka, gama Ubangiji ya faɗa, masifa za ta same ka.”
23 Sai Zadakiya ɗan Kena'ana, ya matso ya mari Mikaiya a kumatu ya ce, “Ta wace hanya ruhun Ubangiji ya fita daga gare ni ya zo ya yi magana da kai.”
24 Mikaiya kuwa ya ce, “Za ka gani a ranar da ka shiga ƙuryar ɗaki na can ciki don ɓuya.”
25 Sai Sarkin Isra'ila ya ce, “Ku kama Mikaiya, ku komar da shi wurin Amon mai mulkin birnin, da yarima Yowash.