7 Allah ya ƙaddara hallakar Ahaziya ta zo ta wurin ziyarar da ya kai wa Yehoram. Gama sa'ad da ya zo, sai ya fita tare da Yehoram don su yi yaƙi da Yehu ɗan Nimshi, wanda Ubangiji ya keɓe don ya kakkaɓe gidan Ahab.
8 Sa'ad da Yehu yake hukunta wa gidan Ahab, sai ya gamu da sarakunan Yahuza, da 'ya'yan 'yan'uwan Ahaziya, maza, suna yi wa Ahaziya hidima, sai ya karkashe su.
9 Ya kuma sa aka nemi Ahaziya. Aka kamo shi sa'ad da ya ɓuya a Samariya, suka kawo shi wurin Yehu, suka kashe shi, suka binne shi, gama suka ce, “Shi jikan Yehoshafat ne wanda ya nemi Ubangiji da zuciya ɗaya.”Don haka a gidan Ahaziya ba wanda ya isa ya riƙe mulkin.
10 Da Ataliya tsohuwar Ahaziya ta ga ɗanta ya mutu, sai ta tashi ta karkashe duk 'yan sarautar gidan Yahuza.
11 Amma sai Yehosheba, 'yar sarki Yoram, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya, ta sace shi daga cikin 'ya'yan sarki waɗanda aka kashe su ta sa shi da mai renonsa a ɗakin kwana. Haka fa, Yehosheba 'yar sarki Yoram, matar Yehoyada firist, ta yi, gama ita 'yar'uwar Ahaziya ce, ta ɓoye Yowash don kada Ataliya ta kashe shi.
12 Yowash yana ɓoye a Haikalin Allah har shekara shida, a lokacin da Ataliya take mulkin ƙasar.