4 Azariya ya yi abin da yake daidai saboda Ubangiji, bisa ga dukan irin abin da tsohonsa Amaziya ya aikata.
5 Ya mai da hankalinsa ga bin Ubangiji a kwanakin Zakariya, wanda ya koya masa tsoron Allah. Dukan lokacin da yake bin Ubangiji, Allah ya wadata shi.
6 Azariya kuwa ya tafi ya yi yaƙi da Filistiyawa, ya rushe garun Gat, da na Yamniya, da na Ashdod. Ya giggina birane a ƙasar Ashdod, da waɗansu wurare na Filistiyawa.
7 Allah ya taimake shi a kan Filistiyawa, da Larabawa, waɗanda suke zaune a Gur-ba'al, da kuma Me'uniyawa.
8 Ammonawa kuma suka kawo masa haraji, sunan Azariya ya kai har kan iyakar Masar, gama ya shahara ƙwarai.
9 Banda haka kuma, Azariya ya gina hasumiyai a Urushalima a Ƙofar Kusurwa, da Ƙofar Kwari, da kan kusurwa, ya kuma yi musu kagara.
10 Ya kuma gina hasumiyai a jeji, ya haƙa tafukka masu yawa, saboda yana da garkunan dabbobi da yawa, da waɗanda suke Shefela da waɗanda suke a filin tudu. Yana kuma da manoma da masu yi wa kurangar inabi aski a tuddai, da wajen ƙasashe masu dausayi, gama shi mai son noma ne ƙwarai.