5 Ya yi yaƙi da Sarkin Ammonawa, ya kuwa ci nasara, har Ammonawa suka ba shi talanti ɗari na azurfa a wannan shekara, da alkama mudu dubu goma (10,000) da sha'ir mudu dubu goma (10,000). Haka Ammonawa suka yi ta biya a shekara ta biyu da ta uku.
6 Yotam ya shahara, saboda ya daidaita al'amuransa a gaban Ubangiji Allahnsa.
7 Sauran ayyukan Yotam, da dukan yaƙe-yaƙensa da al'amuransa, an rubuta su a littafin sarakunan Isra'ila da na Yahuza.
8 Ya ci sarauta, yana da shekara ashirin da biyar, ya kuma yi shekara goma sha shida yana mulki a Urushalima.
9 Sai Yotam ya rasu, suka binne shi a birnin Dawuda. Ahaz ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.