3 A shekara ta takwas ta mulkinsa, a lokacin yana yaro, sai ya fara neman Allah na kakansa Dawuda. A shekara ta goma, sha biyu, sai ya fara tsarkake Yahuza da Urushalima daga masujadai, da Ashtarot, da sassaƙaƙƙun siffofi, da siffofi na zubi.
4 Sai suka farfashe bagadai na Ba'al a gabansa, ya kuma tumɓuke bagadan ƙona turare waɗanda suke a bisansu. Ya ragargaza Ashtarot, da sassaƙaƙƙun siffofi, da na zubi, ya maishe su ƙura. Ya barbaɗa su a kan kaburbura waɗanda suka miƙa hadayu a kansu.
5 Ya kuma ƙone ƙasusuwan firistoci a bisa bagadansu, ya tsarkake Yahuza da Urushalima.
6 A biranen Manassa, da na Ifraimu, da na Saminu, har zuwa Naftali, a kangwayensu kewaye da su,
7 ya farfashe bagadai, ya buge Ashtarot da siffofi, ya maishe su gari, ya tumɓuke dukan bagadan ƙona turare a dukan ƙasar Isra'ila, sa'an nan ya koma Urushalima.
8 A shekara ta goma sha takwas ta mulkinsa, bayan da ya gama tsarkake ƙasar, da Haikalin, sai ya aiki Shafan ɗan Azaliya, da Ma'aseya mai mulkin birnin, da Yowa ɗan Yowahaz, wanda suke magatakarda domin su gyara Haikalin Ubangiji Allahnsa.
9 Sai suka zo wurin Hilkiya babban firist, suka ba shi kuɗin da aka kawo a Haikalin Allah, wanda Lawiyawa, masu tsaron ƙofa, suka tattara daga mutanen Manassa da na Ifraimu, daga sauran Isra'ila, da kuma na dukan Yahuza da Biliyaminu, tare da na mazaunan Urushalima.