1 Yosiya kuwa ya yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji a Urushalima. A rana ta goma sha huɗu ga wata na fari suka yanka ragon Idin Ƙetarewa.
2 Ya sa firistoci a matsayinsu, ya ƙarfafa su a hidimar Haikalin Ubangiji.
3 Ya kuma faɗa wa Lawiyawa, tsarkakakku na Ubangiji, waɗanda suke koya wa dukan Isra'ila, ya ce, “Ku sa tsattsarkan akwatin alkawari a Haikalin da Sulemanu ɗan Dawuda, Sarkin Isra'ila, ya gina. Ba za ku sāke ɗaukarsa bisa kafaɗunku ba. Yanzu fa sai ku kama hidimar Ubangiji Allahnku da jama'arsa Isra'ila.
4 Ku karkasa kanku bisa ga gidajen kakanninku ƙungiya ƙungiya, ku bi bayanin Dawuda, Sarkin Isra'ila, da na ɗansa Sulemanu.
5 Ku tsaya a Wuri Mai Tsarki, bisa ga ƙungiyoyin gidajen kakannin 'yan'uwanku, waɗanda su ba firistoci ba ne. Kowanne ya sami kashi daga cikin gidan Lawiyawa.