1 Ya yi bagade na tagulla, tsawonsa kamu ashirin ne, fāɗinsa kuma kamu ashirin, tsayinsa kuwa kamu goma.
2 Ya yi kwatarniya kewayayyiya ta zubi, kamu goma daga gāɓa zuwa gāɓa, tsayinsa kuwa kamu biyar ne, da'irarsa kuwa kamu talatin.
3 A ƙashiyar kwatarniya akwai siffofin bijimai kamu goma kewaye da ita har jeji biyu. Gaba ɗaya aka yi zubinsu da na kwatarniya.
4 Kwatarniya tana bisa bijimai goma sha biyu, uku suna fuskantar gabas, uku suna fuskantar yamma, uku suna fuskantar kudu, uku kuma suna fuskantar arewa. Kwatarniya tana bisa bijiman, gindin kowannensu yana daga ciki.