7 Sa'an nan ya yi alkuki goma na zinariya kamar yadda aka tsara. Ya sa su cikin Haikali, biyar a sashen dama, biyar kuma a hagu.
8 Ya kuma yi tebur goma, ya ajiye a cikin Haikalin, biyar a dama, biyar kuma a hagu. Ya kuma yi kwanonin zinariya guda ɗari.
9 Sa'an nan ya yi wani shirayi domin firistoci, ya kuma yi wani babban shirayi, ya yi ƙofofi domin shirayun. Ya dalaye ƙyamaren ƙofofin da tagulla.
10 Ya girka kwatarniya a kusurwar kudu maso gabas daura da Haikalin.
11-16 Huram kuma ya yi tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da daruna. Huram kuwa ya gama dukan aikin da ya alkawarta wa sarki Sulemanu a Haikalin Allah:ginshiƙi biyudajiya biyu a kan ginshiƙi biyusiffar tukakkiyar sarƙa a kan kowane ginshiƙiSiffar rumman guda ɗari huɗu domin raga don rufe dajiyar ginshiƙandakali gomadaro gomakwatarniyabijimi goma sha biyu da suke ɗauke da kwatarniyakwanoni, manyan cokula masu yatsotsi, wato ya yi dukan kayan nan da tagulla domin haikalin Ubangiji
17 Sarki ya yi zubinsu a filin Urdun tsakanin Sukkot da Zaretan a wuri mai yumɓu.
18 Haka Sulemanu ya yi kayayyakin nan da yawa ƙwarai, har ba a iya lissafin yawan nauyin tagullar da aka yi amfani da ita ba.