17 Saboda haka, ya Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka tabbatar da maganarka wadda ka yi wa bawanka Dawuda.
18 “Ashe kuwa Allah zai zauna tare da ɗan adam a duniya? Ga shi kuwa, sama da saman sammai ba su iya ɗaukarka ba, balle fa ɗakin da na gina.
19 Duk da haka ka kula da addu'ar bawanka da roƙe-roƙensa. Ya Ubangiji Allahna, ka kasa kunne ga kuka da addu'ar da bawanka yake yi a gabanka.
20 Ka dubi wajen Haikalin nan dare da rana, wurin da ka yi alkawari za ka sa sunanka, ka kasa kunne ga addu'ar da bawanka zai yi wajen wannan wuri,
21 ka ji roƙe-roƙen bawanka da na jama'ar Isra'ila, sa'ad da suke addu'a suna fuskantar wannan wuri, ka ji daga wurin da kake zaune a Sama, sa'ad da ka ji, ka gafarta.
22 “Idan wani ya yi wa maƙwabcinsa laifi, har aka sa shi ya rantse, ya kuwa zo ya rantse a gaban bagaden a wannan Haikali,
23 sai ka ji ka yi wa bayinka shari'a daga Sama, ka hukunta wa mugun, ka ɗora masa alhakinsa, ka baratar da adalin, ka ba shi sakayyar adalcinsa.