20 Ka dubi wajen Haikalin nan dare da rana, wurin da ka yi alkawari za ka sa sunanka, ka kasa kunne ga addu'ar da bawanka zai yi wajen wannan wuri,
21 ka ji roƙe-roƙen bawanka da na jama'ar Isra'ila, sa'ad da suke addu'a suna fuskantar wannan wuri, ka ji daga wurin da kake zaune a Sama, sa'ad da ka ji, ka gafarta.
22 “Idan wani ya yi wa maƙwabcinsa laifi, har aka sa shi ya rantse, ya kuwa zo ya rantse a gaban bagaden a wannan Haikali,
23 sai ka ji ka yi wa bayinka shari'a daga Sama, ka hukunta wa mugun, ka ɗora masa alhakinsa, ka baratar da adalin, ka ba shi sakayyar adalcinsa.
24 “Idan abokan gāba sun kori jama'arka, wato Isra'ila, saboda laifin da suka yi maka, sa'an nan suka juyo suka shaida sunanka, suka yi addu'a, suka yi roƙo a gabanka a wannan Haikali,
25 sai ka ji daga Sama ka gafarta zunubin jama'arka Isra'ila, ka komo da su ƙasar da ka ba su, su da kakanninsu.
26 “Sa'ad da aka kulle sammai, ba ruwan sama saboda sun yi maka zunubi, sa'an nan suka fuskanci wurin nan suka yi addu'a, suka shaida sunanka, suka juyo suka daina zunubinsu a sa'ad da ka hukunta su,