16 Yanzu fa na riga na zaɓi wannan Haikali, na kuwa keɓe shi domin sunana ya kasance a wurin har abada. Idanuna da zuciyata kuma za su kasance a wurin kullayaumin.
17 Amma kai, idan za ka yi zamanka a gabana kamar yadda tsohonka Dawuda ya yi, ka kuma aikata bisa ga dukan abin da na umarce ka, ka kiyaye dokokina da farillaina,
18 to, zan kafa gadon sarautarka, yadda na alkawarta wa tsohonka Dawuda, cewa ba za a rasa mutumin da zai yi mulkin Isra'ila ba.
19 Amma idan ka juya, ka bar dokokina da umarnaina waɗanda na sa a gabanka, har ka shiga bautar gumaka kana musu sujada,
20 to, sai in tumɓuke ka daga ƙasata wadda na ba ka, wannan Haikali kuma wanda na riga na keɓe domin sunana, zan kawar da shi daga fuskata, zan kuwa maishe shi abin karin magana, abin raini ga dukan sauran al'umma.
21 “Haikali kuwa, wanda aka ɗaukaka, duk mai wucewa zai yi mamaki ya ce, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi wa wannan ƙasa da wannan Haikali haka?’
22 “Sa'an nan kuma za su ce, ‘Saboda sun rabu da Ubangiji, Allah na kakanninsu, wanda ya fitar da su daga ƙasar Masar, amma suka bi waɗansu gumaka, suka yi musu sujada, suka bauta musu, saboda haka ne ya aukar musu da duk wannan bala'i.’ ”