2 sa'an nan ya sāke giggina biranen da Hiram ya ba shi, ya zaunar da Isra'ilawa a cikinsu.
3 Sai Sulemanu ya tafi ya ci Hamat-zoba da yaƙi.
4 Sa'an nan ya gina Tadmor a jeji, a Hamat kuwa ya gina biranen ajiya.
5 Ya kuma gina Bet-horon ta kan tudu da Bet-horon ta kwari, birane masu kagara kuwa ya gina musu garu, da ƙofofi, da ƙyamare,
6 da kuma Ba'alat da dukan biranen ajiya waɗanda yake da su, da birane don karusansa, da birane don mahayan dawakansa, ya gina dukan abin da yake bukata a Urushalima, da Lebanon, da a dukan ƙasashen da suke cikin mulkinsa.
7 Dukan jama'ar da suka ragu a ƙasar, wato Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, waɗanda Isra'ilawa ba su hallaka ba,
8 daga cikin zuriyarsu waɗanda suka ragu a ƙasar a bayansu, waɗanda Isra'ilawa ba su hallaka ba, su ne Sulemanu ya tilasta su biya gandu, haka kuwa suke har wa yau.