1 Ga zantuttukan Amos, ɗaya daga cikin makiyayan ƙauyen Tekowa. Allah ya bayyana wa Amos wannan saƙo, tun shekara biyu kafin girgizar duniya, a lokacin da Azariya yake sarautar Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash kuwa yake sarautar Isra'ila.
2 Amos ya ce,“Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona,Muryarsa za ta yi tsawa dagaUrushalima.Da jin wannan, sai wuraren kiwo zasu bushe,Ƙwanƙolin Dutsen Karmel, da yakekore zai yi yaushi.”
3 Ubangiji ya ce,“Mutanen Dimashƙu sun ci gaba dayin zunubi.Hakika, zan hukunta su,Don sun zalunci mutanen Gileyad dazalunci mai tsanani.
4 Don haka zan aukar da wuta a kanfādar Sarkin Suriya.Za ta ƙone kagarar Ben-hadad,sarki.