1 Jama'ar Isra'ila, ku kasa kunne ga wannan saƙo da Ubangiji ya aiko muku, ya ce, “Na fitar da iyalanku duka daga Masar.
2 Daga cikin dukan al'umman da nakeƙauna a duniya,Ku kaɗai ne na sani,Nake kuma kulawa da ku,Don haka zan hukunta ku sabodazunubanku.”
3 Zai yiwu a ce mutum biyu za su yitafiya tare,Amma su rasa shirya magana?
4 Zai yiwu zaki yă yi ruri a jejiBa tare da ya kama nama ba?Zai yiwu sagarin zaki yă yi gurnani akogonsaIn bai kama wani abu ba?