1 Jama'ar Isra'ila, ku kasa kunne ga wannan saƙo da Ubangiji ya aiko muku, ya ce, “Na fitar da iyalanku duka daga Masar.
2 Daga cikin dukan al'umman da nakeƙauna a duniya,Ku kaɗai ne na sani,Nake kuma kulawa da ku,Don haka zan hukunta ku sabodazunubanku.”
3 Zai yiwu a ce mutum biyu za su yitafiya tare,Amma su rasa shirya magana?
4 Zai yiwu zaki yă yi ruri a jejiBa tare da ya kama nama ba?Zai yiwu sagarin zaki yă yi gurnani akogonsaIn bai kama wani abu ba?
5 Zai yiwu tsuntsu ya fāɗi ƙasaIn ba a kafa masa tarko ba?Zai yiwu tarko ya zarguIn bai kama wani abu ne ba?
6 Zai yiwu mutane su rasa firgita,Idan aka busa ƙahon yaƙi abirni?Zai yiwu wata babbar masifa ta aukowa birniBa da yardar Ubangiji ba?
7 Hakika Ubangiji ba yakan aikatakome ba,Sai da sanin bayinsa annabawa.