3 Zai yiwu a ce mutum biyu za su yitafiya tare,Amma su rasa shirya magana?
4 Zai yiwu zaki yă yi ruri a jejiBa tare da ya kama nama ba?Zai yiwu sagarin zaki yă yi gurnani akogonsaIn bai kama wani abu ba?
5 Zai yiwu tsuntsu ya fāɗi ƙasaIn ba a kafa masa tarko ba?Zai yiwu tarko ya zarguIn bai kama wani abu ne ba?
6 Zai yiwu mutane su rasa firgita,Idan aka busa ƙahon yaƙi abirni?Zai yiwu wata babbar masifa ta aukowa birniBa da yardar Ubangiji ba?
7 Hakika Ubangiji ba yakan aikatakome ba,Sai da sanin bayinsa annabawa.
8 Zaki ya yi ruri!Wa ba zai ji tsoro ba?Sa'ad da Ubangiji ya yi magana!Wa zai ƙi yin shelar maganarsa?
9 Ka yi shela ga mazaunan fādar Ashdod da Masar, ka ce, “Duk ku taru a Samariya ku ga irin babban shashancin da ake yi a can, ku ga irin laifofin da ake aikatawa a birnin.”