5 Kada ku tafi ku yi sujada a Biyer-sheba.Kada ku yi ƙoƙarin nemana aBetel,Gama Betel lalacewa za ta yi.Kada ku tafi Gilgal,Gama an ƙaddara wa jama'arta suyi ƙaura.”
6 Ku tafi wurin Ubangiji ku tsira.Idan kuwa kun ƙi,Shi zai babbaka jama'ar YusufuKamar yadda a kan babbaka dawuta.Wuta za ta ƙone jama'ar Betel,Ba kuwa mai kashe wutar.
7 Abin tausayi ne ku da kuke ɓatashari'a,Kuna hana wa mutane hakkinsu.
8 Ubangiji ne ya yi taurarinKaza da 'ya'yantaDa mai farauta da kare.Ya mai da duhu haske,Rana kuwa dare.Shi ya kirawo ruwan teku yabayyana,Ya shimfiɗa shi a bisa ƙasa.Sunansa Ubangiji ne.
9 Ya kawo halaka a kan ƙarfafa,Da a kan birane masu garu.
10 Kun ƙi wanda ya tsaya a kanadalci,Da mai faɗar ainihin gaskiya a gabanshari'a.
11 Kun matsa wa talakawa lamba,Kun ƙwace musu abincinsu.Saboda haka kyawawan gidajen nanda kun gina da dutse,Ba za ku zauna a cikinsu ba,Ba kuwa za ku sha ruwan inabinnanDaga kyawawan gonakin inabinkuba.