10 Sa'ad da dangin mamacin ya shiga don ya fitar da gawar, ya ƙone, sai ya yi kira ga ko wane ne da yake ɓoye a gidan, ya ce, “Ko akwai wani kuma a nan?”Sai a amsa, “A'a.”Zai ce, “Kul! Kada a ambaci sunan Ubangiji.”
11 Sa'ad da Ubangiji ya ba da umarni, babban gida da ƙarami rushewa za su yi.
12 Dawakai sukan yi sukuwa aduwatsu?Ana huɗan teku da garmarshanu?Duk da haka kuka mai da adalcidafi,Kuka mai da nagarta, mugunta.
13 Kuna fariyar cin garin Lodebar, watowofi, da yaƙi.Kun ce, “Ƙarfinmu ya isa har mu ciKarnayim, wato ƙaho biyu, dayaƙi.”