1 Ubangiji ya nuna mini wahayi, sai na ga kwandon ɓaure na ci.
2 Sai Ubangiji ya ce, “Amos, me ka gani?”Na ce, “Kwandon ɓaure na ci.”Ubangiji kuma ya ce mini, “Ƙarshen jama'ata Isra'ila ya zo. Ba zan sāke nufina a kan yi musu hukunci ba.
3 Waƙoƙin da akan raira a fāda, za su zama na makoki a wannan rana. Za a iske gawawwaki ko'ina. Ba za a ji motsin kome ba.”
4 Ku ji wannan, ku da kuke tattake masu bukata, kuna ƙoƙari ku hallakar da matalautan ƙasar.