1 Akwai wani mutum a ƙasar Uz, mai suna Ayuba, amintacce ne, mai tsoron Allah. Shi mutumin kirki ne, natsattse, yana ƙin aikata kowace irin mugunta.
2 Yana da 'ya'ya bakwai maza, uku mata.
3 Yana da tumaki dubu bakwai (7,000), da raƙuma dubu uku (3,000), da shanu dubu guda (1,000), da jakuna ɗari biyar. Yana kuma da barori masu yawan gaske, don haka ya fi kowa a ƙasar gabas arziki nesa.
4 'Ya'yansa maza sukan yi liyafa bi da bi a gidajen junansu, inda su duka sukan taru koyaushe, sukan gayyaci 'yan'uwan nan nasu mata su halarci liyafar.
5 A kowane lokacin da aka gama da liyafar, Ayuba yakan tashi da sassafe, kashegarin liyafar, yă miƙa hadayu don yă tsarkake 'ya'yansa. Haka yake yi kullum, don yana zaton mai yiwuwa ne ɗaya daga cikin 'ya'yan ya yi zunubi, ya saɓi Allah a ɓoye.