7 Sai Ubangiji ya tambaye shi, ya ce, “Kai fa me kake yi?”Shaiɗan ya amsa, ya ce, “Ina ta kaiwa da kawowa ne, a ko'ina a duniya.”
8 Ubangiji ya ce masa, “Ko ka lura da bawana Ayuba? Ba wani mutumin kirki, mai aminci, kamarsa a duniya. Yana yi mini sujada, natsattse ne, yana ƙin aikata kowace irin mugunta.”
9 Shaiɗan ya amsa, ya ce, “A banza Ayuba yake yi maka sujada?
10 Ai, don ka kiyaye shi ne, shi da iyalinsa, da dukan abin da yake da shi. Ka kuma sa wa duk abin da yake yi albarka, ka kuwa ba shi shanun da suka isa su cika dukan ƙasan nan.
11 Amma da a ce za ka raba shi da dukan abin hannunsa, to, da zai fito fili yă zage ka ƙiri ƙiri.”
12 Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, dukan abin hannunsa yana cikin ikonka, amma shi kansa kada ka cuce shi.” Sai Shaiɗan ya tafi.
13 Wata rana 'ya'yan Ayuba suna shagali a gidan wansu,