8 “Da ikonka ne ka yi ni, ka siffata ni,Yanzu kuma da ikon nan naka ne za ka hallaka ni.
9 Ka tuna, ya Allah, kai ka halicce ni, da yumɓu kuwa ka yi ni.Za ka murtsuke ni ne, in kuma koma ƙura?
10 Kai ne ka ba mahaifina ƙarfin da zai haife ni,Kai ne ka sa na yi girma a cikin cikin mahaifiyata.
11 Kai ne ka siffata jikina da ƙasusuwa da jijiyoyi,Ka rufe ƙasusuwan da nama, naman kuma ka rufe da fata.
12 Kai ne ka ba ni rai da madawwamiyar ƙauna,Kulawarka ce ta sa ni rayuwa.
13 Amma yanzu na sani,Dukan lokacin nan kana da wani nufi a ɓoye game da ni.
14 Jira kake ka ga ko zan yi zunubi,Don ka ƙi gafarta mini.