3 Ayuba,kana tsammani ba za mu iya ba ka amsa ba?Kana tsammani maganganunka na ba'aZa su sa mu rasa abin da za mu mayar maka?
4 Ka ɗauka duk abin da kake faɗa gaskiya ne,Ka kuma mai da kanka kai mai tsarki ne a gaban Allah.
5 Da ma Allah zai amsa maka,Ya yi magana gāba da kai,
6 Da ya faɗa maka hikima tana da fannoni da yawa.Akwai abubuwa waɗanda suka fi ƙarfin ganewar ɗan adam.Duba, Allah ya ƙyale wani ɓangare na laifinka.
7 “Kana iya gane matuƙa da iyakarGirman Allah da na ikonsa?
8 Sararin sama ba shi ne matuƙa a wurin Allah ba,Amma ga shi, yana can nesa da kai,Allah ya san lahira,Amma kai ba ka sani ba.
9 Fāɗin girman Allah ya fi duniyaYa kuma fi teku fāɗi.