1 Ayuba ya amsa.
2 “Aha! Ashe, kai ne muryar jama'a,Idan ka mutu hikima ta mutu ke nan tare da kai.
3 Amma ni ma ina da hankali gwargwado, kamar yadda kake da shi,Ban ga yadda ka fi ni ba.Kowa ya san sukan abin da ka faɗa.
4 Har abokaina ma, suna ta yi mini dariya yanzu,Suna ta dariya ko da yake ni adali ne marar laifi,Amma akwai lokacin da Allah ya amsa addu'o'ina.