4 Har abokaina ma, suna ta yi mini dariya yanzu,Suna ta dariya ko da yake ni adali ne marar laifi,Amma akwai lokacin da Allah ya amsa addu'o'ina.
5 Ba ka shan wahalar kome, duk da haka ka maishe ni abin dariya.Ka bugi mutumin da yake gab da fāɗuwa.
6 Amma ɓarayi da marasa tsoronAllah suna zaune cikin salama,Ko da yake ƙarfinsu ne kaɗai allahnsu.
7 “Don haka tsuntsaye da dabbobi sun fi ka sani,Suna da abu mai yawa da za su koya maka.
8 Ka roƙi talikan da suke a duniya, da cikin teku, hikimar da suke da ita.
9 Dukansu sun sani ikon Ubangiji ne ya yi su.
10 Allah shi ne yake bi da rayukan talikansa.Numfashin dukan mutane kuwa a ikonsa yake.