10 Ko da yake kun ɓoye son zuciyarku,Duk da haka zai tsauta muku,
11 Ikonsa kuwa zai razana ku.
12 Karin maganarku da muhawararku ba su da ƙarfi ƙwarai.
13 “Ku yi shiru ku ba ni zarafi in yi magana.Duk abin da zai faru, ya faru.
14 A shirye nake in yi kasai da raina.
15 Na fid da zuciya ɗungum.To, in Allah ya kashe ni, sai me?Zan faɗa masa ƙarata.
16 Mai yiwuwa ne ƙarfin halina ya cece ni,Tun da yake ba wani mugun mutumin da zai iya zuwa gaban Allah.