1-2 “Duk abin da ka hurta, na taɓa jinsa,Na gane da shi sarai.Iyakar abin da kuka sani, ni ma na sani.Ba ku fi ni da kome ba.
3 Amma da Allah nake jayayya, ba da ku ba,Ina so in yi muhawara da shi a kan ƙarar da nake da ita.
4 Kun ɓoye jahilcinku da ƙarairayi.Kun zama kamar likitoci waɗanda ba su iya warkar da kowa ba.
5 Kada ku faɗi kome,Wani sai ya ce kuna da hikima!
6 “Ku saurara mini, zan faɗi ƙarata.
7 Me ya sa kuke yin ƙarya?Kuna tsammani ƙarairayinku za su taimaki Allah?