5 Kada ku faɗi kome,Wani sai ya ce kuna da hikima!
6 “Ku saurara mini, zan faɗi ƙarata.
7 Me ya sa kuke yin ƙarya?Kuna tsammani ƙarairayinku za su taimaki Allah?
8 Son zuciya kuke yi, ko ba haka ba?Kuna goyon bayan Allah?Za ku goyi bayan Allah sa'ad da aka gurfanar da ni gaban shari'a?
9 Da Allah ya bincike ku sosai,Zai iske wani abin kirki ne a cikinku?Kuna tsammani za ku ruɗi Allah, kamar yadda kuke ruɗin mutane?
10 Ko da yake kun ɓoye son zuciyarku,Duk da haka zai tsauta muku,
11 Ikonsa kuwa zai razana ku.