1 “Mutum duka kwanakin ransa gajere ne, kwanakin wahala kuwa.
2 Sukan yi girma su bushe nan da nan kamar furanni,Sukan shuɗe kamar inuwa.
3 Na ma isa ka dube ni ne, ya Allah?Ko ka gabatar da ni a gabanka,Ka yi mini shari'a?
4 Ba wani abu tsarkakakkeDa zai fito daga cikin kowane marar tsarki, kamar mutum.
5 Tsawon kwanakin ransa, an ƙayyade su tun can,An ƙayyade yawan watannin da zai yi,Ka riga ka yanke haka ya Allah, ba su sākuwa.