4 Ba wani abu tsarkakakkeDa zai fito daga cikin kowane marar tsarki, kamar mutum.
5 Tsawon kwanakin ransa, an ƙayyade su tun can,An ƙayyade yawan watannin da zai yi,Ka riga ka yanke haka ya Allah, ba su sākuwa.
6 Ka kawar da fuska daga gare shi, ka rabu da shi,Ka bar shi ya ji daɗin kwanakinsa na fama da aiki idan zai iya.
7 “Akwai sa zuciya ga itacen da aka sare,Yana iya sāke rayuwa ya yi toho.
8 Ko da yake saiwoyinsa sun tsufa,Kututturensa kuma ya ruɓe a ƙasa,
9 In aka zuba ruwa, sai ya toho kamar sabon tsiro.
10 Amma ɗan mutum ya mutu, ƙarshensa ke nan,Ya mutu, a ina yake a lokacin nan?