19 Ƙasaru 'yantacciya ce daga baƙiBa wanda zai raba su da Allah.
20 “Mugun mutum mai zaluntar sauran mutaneZai kasance da wahala muddin ransa.
21 Zai ji ƙarar muryoyi masu firgitarwa a kunnuwansa.'Yan fashi za su fāɗa masaSa'ad da yake tsammani ba abin da zai same shi.
22 Bai sa zuciya zai kuɓuta daga duhu ba,Gama takobi yana jiransa a wani wuri don ya kashe shi.
23 Yana ta yawon neman abinci, yana ta cewa, ‘Ina yake?’Ya sani baƙin ciki ne yake jiransa a nan gaba. Kamar sarki mai iko,
24 Haka masifa take shirin fāɗa masa.
25 “Wannan shi ne ƙaddarar mutum,Wanda ya nuna wa Allah yatsa,Ya kuwa raina Mai Iko Dukka.