2 “Surutai, Ayuba! Surutai!
3 Ba wani mai hikima wanda zai yi magana irin taka,Ko kuma ya kāre kansa da irin maganganun da ba su da ma'ana.
4 Kana karya jama'a, kana hana su jin tsoron Allah,Kana hana su yin addu'a gare shi.
5 Mugun lamirinka shi ne yake magana yanzu,Kana ƙoƙari ka ɓuya a bayan maganganunka na wayo.
6 Ba na bukata in kā da kai,Kowace kalma da ka hurta ta kā da ka.
7 “Kana tsammani kai ne mutumin da aka haifa na farko?Sa'ad da Allah ya yi duwatsu kana nan?
8 Ko ka taɓa jin shirye-shiryen da Allah ya yi?Ko kai kaɗai kake da hikima a cikin mutane?