19 Akwai wani a SamaWanda zai tsaya mini ya goyi bayana.
20 Ina so Allah ya ga hawayena,Ya kuma ji addu'ata.
21 “Ina so wanda zai yi roƙo ga Allah domina,Kamar yadda mutum yakan yi roƙo domin abokinsa.
22 Yanzu shekaruna wucewa suke yi,Ina bin hanyar da ba a komawa.”