5 Da sai in ba ka shawara ta ƙarfafawa,In yi ta yi maka maganar ta'azantarwa.
6 “Amma ba abin da zan faɗa wanda zai taimaka,Yin shiru kuma ba zai raba ni da azaba ba.
7 Ka gajiyar da ni, ya Allah,Ka shafe iyalina.
8 Ka kama ni, kai maƙiyina ne.Na zama daga fata sai ƙasusuwa,Mutane suka ɗauka, cewa wannan ya tabbatar ni mai laifi ne.
9 Allah ya kakkarya gaɓoɓina da fushinsa,Yana dubana da ƙiyayya.
10 Mutane sun buɗe baki don su haɗiye niSuna kewaye ni suna ta marina.
11 Allah ya bashe ni ga mugaye.