1 “Ƙarshen raina ya gabato, da ƙyar nake numfashi,Ba abin da ya rage mini sai kabari.
2 Na lura da yadda mutane suke yi mini mummunar ba'a.
3 Ni amintacce ne, ya Allah, ka yarda da maganata.Ba wanda zai goyi bayan abin da nake faɗa.
4 Ka baƙantar da hankalinsu, ya Allah,Kada ka bar su su yi mini duban wulakanci yanzu.
5 A karin maganar mutanen dā an ce,‘Kowa ya ci amanar abokinsa saboda kuɗi,'Ya'yansa sā sha wahala!’
6 Yanzu kuwa sun mai da wannan karin magana a kaina.Da mutane suka ji,Suka zo suka yi ta tofa mini yau a fuska.