11 “Kwanakina sun ƙare, shirye-shiryena sun kāsa,Ba ni da sauran sa zuciya.
12 Amma abokaina sun ce dare shi ne hasken rana,Sun kuma ce haske yana kusa,Ko da yake ina cikin duhu.
13 Ba ni da sauran sa zuciya,Gidana yana lahira,Inda zan kwanta in yi ta barci cikin duhu.
14 Zan ce kabari shi ne mahaifina,Tsutsotsin da suke cinye ni su ne mahaifiyata, da 'yan'uwana mata.
15 Ina ne zan sa zuciyata?Wane ne ya ga inda zan sa ta?
16 Akwai wanda ya yi shiri a binne shi tare da ni,Mu tafi tare da shi zuwa lahira?”