3 Ni amintacce ne, ya Allah, ka yarda da maganata.Ba wanda zai goyi bayan abin da nake faɗa.
4 Ka baƙantar da hankalinsu, ya Allah,Kada ka bar su su yi mini duban wulakanci yanzu.
5 A karin maganar mutanen dā an ce,‘Kowa ya ci amanar abokinsa saboda kuɗi,'Ya'yansa sā sha wahala!’
6 Yanzu kuwa sun mai da wannan karin magana a kaina.Da mutane suka ji,Suka zo suka yi ta tofa mini yau a fuska.
7 Baƙin cikina ya kusa makantar da ni,Hannuwana da ƙafafuna sun rame,sun zama kamar kyauro.
8 Duk waɗanda suka zaci su adalai ne sun razana.Dukansu sun kāshe ni, cewa ni ba mai tsoron Allah ba ne.
9 Har su ma da suke cewa su mutanen kirki neSuna ƙara tabbatarwa ba su yi kuskure ba.