6 Yanzu kuwa sun mai da wannan karin magana a kaina.Da mutane suka ji,Suka zo suka yi ta tofa mini yau a fuska.
7 Baƙin cikina ya kusa makantar da ni,Hannuwana da ƙafafuna sun rame,sun zama kamar kyauro.
8 Duk waɗanda suka zaci su adalai ne sun razana.Dukansu sun kāshe ni, cewa ni ba mai tsoron Allah ba ne.
9 Har su ma da suke cewa su mutanen kirki neSuna ƙara tabbatarwa ba su yi kuskure ba.
10 Amma da a ce dukansu za su zo su tsaya a gabana,Da ba zan sami mai hikima ko ɗaya daga cikinsu ba.
11 “Kwanakina sun ƙare, shirye-shiryena sun kāsa,Ba ni da sauran sa zuciya.
12 Amma abokaina sun ce dare shi ne hasken rana,Sun kuma ce haske yana kusa,Ko da yake ina cikin duhu.