13 Mummunan ciwo ya bazu ko'ina a jikinsa,Yana sa hannuwansa da ƙafafunsa su ruɓe,
14 Dā yana zaune lafiya,Sai razana ta tatike shi,Ta jawo shi zuwa ga Sarkin Mutuwa.
15 Yanzu kowa zai iya zama a alfarwarsa,Bayan da an karkashe ƙwayoyin cuta da farar wuta.
16 Saiwoyinsa da rassansa suka yi yaushi suka bushe.
17 Sunansa ya ƙare a gida da a jeji,Ba wanda yake ƙara tunawa da shi.
18 Za a kore shi daga ƙasar masu rai,Za a kore shi daga haske zuwa duhu.
19 Ba shi da zuriya, da sauran waɗanda suka ragu da rai.